Bankin duniya ya bukaci gwamnatin tarayya da kada ta sauya manufofin da aka bullo da su na gyaran tattalin arziki, yana mai gargadin cewa hakan na iya haifar da mummunan tasiri ga kasar.
Kawar da tallafin man fetur da kuma soke tsarin musayar kudaden waje ne manufofin da gwamnati mai ci ne ta bullo da su a rana ta farko da hawan ta mulki.
KARANTA WANNAN MA:Dalilin da ya sa faduwar darajar Naira ta zama alheri ga Nijeriya – Gwamnan CBN
Yayin da gwamnatin tarayya ta ke kare manufofin, da dama daga cikin ‘yan Najeriya na kokawa da irin tasirin da suke da shi ga talakawa.
Daily Trust ta rawaito cewa da ya ke jawabi a wajen kaddamar da rahoton ci gaban Najeriya (NDU) a Abuja a yau Alhamis, darektan bankin duniya a Najeriya, Dr. Ndiame Diop, ya ce duk da cewa sauye-sauyen na iya kawo wahalhalu, sun zama dole domin daidaito kan tattalin arziki.
Diop ya yi gargadin cewa, “Mayar da wadannan sauye-sauyen zai yi illa kuma babbar matsala ce ga Najeriya.”
A nashi bangaren, Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na ci gaba da bijiro da manufofi da ta ke yi.