Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso, ya bayyana cewa mummunan faduwar darajar Naira na ba wa kasar nan damar bunkasa fitar da kayayyaki zuwa wasu kasashen.
Nairametrics ta rawaito cewa Cardoso ya yi wannan bayani ne a taron Tattalin Arzikin Najeriya a jiya Laraba a Abuja.
Gwamnan na CBN ya jaddada cewa rage darajar Naira ya sa kasuwancin fitar da kaya ya zama ya bunƙasa tare da jawo hankalin masu zuba jari da dama da ke amfana da wannan dama.
KARANTA WANNAN MA:Hukumar alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin da maniyyata za su fara biya don aikin Hajjin badi
Cardoso ya amince da cewa duk da cewa halin da ake ciki yanzu ba shi da kyau, yanayin yanzu na samar da dama ga mutane su gane su kuma bi hanyoyin saka hannun jari.
“Idan aka duba fuskar shawo kan mutane, abin da muke bukata a yanzu shi ne tabbatar da cewa saka hannun jari yana nan. Misali, yanzu za a iya ganin wannan a matsayin barazana, duba da yadda darajar naira ta fadi sosai. Amma hakan ma dama ce, domin abin da hakan ke nufi shi ne zai taimaka wajen bunkasa fitar da kayayyaki
“Hakan zai sa Najeriya ta zama kasa mai gasa sosai a fannin kasuwancin fitar da kaya. Ina so in karfafa gwiwar mutane da su fahimci cewa damarmu na nan. Abubuwa suna sauyawa a wata fuska ta musamman. Ba cikakke ba ne, amma tabbas akwai dama ga mutane su gano su kuma zuba jari.
“Lokacin da ka fara fitar da kayayyaki zuwa wasu kasashe tare da kudin shigowa daga nan da kuma Naira da ta yi kasa, za ka ga yanayi inda bukatar kayayyakin ka ya karu sosai. Kuma ina ganin hakan yana faruwa. Wasu suna yin hakan kuma kudin ruwa na kara yawa sosai,” in ji Cardoso.