Ƴansanda a Abuja sun tabbatar da mutuwar mutane goma, inda takwas kuma su ka jikkata a wata turreniya yayin rabon kayan abinci a wata coci a Abuja.
Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya afku ne a safiyar yau Asabar a yayin wani taron raba shinkafa da sauran kayayyakin jin kai da aka gudanar a cocin Holy Trinity ta Katolika da ke unguwar Maitama a Abuja.
Wakilin Daily Trust da ke wurin ya lura da yadda jami’an tsaro suka mamaye wajen.
KARANTA NAN MA: Ɗan Barau Jibrin, Shawall, ya lashe lambar-girma sakamakon taimakon al’umma
An tattaro cewa cocin ta saba rabon tallafi ga al’umma a kowace shekara a irin wannan lokacin.
Wadanda rikicin ya rutsa da su galibi mata ne da yara.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, rundunar ƴansandan babban birnin tarayya Abuja, ta bakin kakakin ta, SP Josephine Adeh, ta ce mutane goma ne suka mutu, yayin da wasu takwas suka samu raunuka daban-daban.