Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) tare da ma’aikatan gwamnatin tarayya sun bukaci gwamnati ta gaggauta sake duba mafi ƙarancin albashi na ƙasa, suna mai cewa naira 70,000 da ake biya a yanzu ya gaza ɗaukar nauyin ma’aikata.
Sakataren riko na NLC, Benson Upah, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki da tsadar sufuri, haya da wutar lantarki sun sa kimar N70,000 ta ragu sosai, inda ma’aikata ke shiga cikin ƙuncin rayuwa.
Ya ce idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, matsalar za ta tsananta.
Haka zalika, shugaban Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati (ASCSN), Shehu Mohammed, ya ce tun farko ƙungiyarsu ta nemi a ɗora mafi ƙarancin albashi kan N250,000, domin N70,000 ba zai iya biyan bukatun ma’aikaci da iyalinsa ba.
Rahotanni sun nuna cewa wasu jihohi sun riga sun ɗaga mafi ƙarancin albashi sama da na ƙasa. A Imo, Gwamna Hope Uzodinma ya amince da N104,000, yayin da Legas da Rivers suka sa N85,000, Bayelsa, Niger, Enugu da Akwa Ibom suka amince da N80,000. Jihohi irin su Ogun, Delta, Benue, Osun da Ondo suma sun ɗaga albashin fiye da N70,000.
Wasu ma’aikatan gwamnati da suka yi magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) sun koka da tsadar rayuwa, suna mai cewa kuɗin da suke samu ba ya isa biyan haya, kuɗin makaranta da abinci. Sun bukaci gwamnatin tarayya ta ɗaga albashi zuwa akalla N150,000 domin farfaɗo da tattalin arziki da kuma inganta jin daɗin ma’aikata.