Kansila mai wakiltar mazabar Kinkiba a karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna, Sunusi Hashim, ya naɗa masu ba shi shawara na musamman 18 domin ƙarfafa shugabancin sa daga tushe.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an kaddamar da masu ba da shawarar a jiya Lahadi a wabi taro da aka shirya a makarantar firamare ta Kinkiba, inda manyan jam’iyyar APC, magoya baya, masu riƙe da sarautar gargajiya, shugabannin addini da al’umma suka halarta.
Hashim ya ce, an yi wannan naɗi ne saboda sadaukarwa, amincewa da kuma gudunmawar da waɗanda aka zaɓa ke bayarwa wajen ci gaban mazaɓar Kinkiba.
ADVERTISEMENT
Ya ƙara da cewa: “Ina roƙon su da su yi aiki cikin girmamawa, gaskiya, amana, gaskiya a bayyane da kuma tausayi ga al’umma.”