BA SALLAH KAƊAI AKE YI A AIKIN HAJJI BA — HAJJI IBADA CE DA AKE YIN TA DA JIKI
Idan ba zaka iya tafiya 5km a Abuja ba tare da tsayawa ba, zaka sha wahala a Makkah.
*Nawa zaka yi tafiya a Hajj? Jimilla: 70-90km cikin kwanaki 5
– Tawaf: 3.5km
– Sa’ee: 3.5km
– Mina zuwa Arafat: 14km
– Arafat zuwa Muzdalifah: 9km
– Muzdalifah zuwa Mina: 7km
– Jamarat (kwanaki 3): 12-15km
– Duk a cikin zafi 40-45°C, cikin Ihram, ba bacci sosai.
ME YA SA MAHAJJATAN NIGERIA KE FADUWA?
1. Shekaru 50-70, ba motsa jiki shekaru 10
2. Sugar, BP, ciwon gwiwa a boye
3. Zafi ya bambanta — daga 28°C Abuja zuwa 45°C Arafat
4. Bacci a kasa a Mina
5. Rashin shan ruwa
Sakamakon: Bugun zafi, kumburin kafa, ciwon zuciya a Arafat.
SHIRIN MOTSA JIKI NA WATANNI 6 —A FARA TUN YANZU, BA MAKO 1 BA
Wata 1-2: Gina Tushe
– Yi tafiya minti 30 kowace rana, kwanaki 5 a mako, da safe
– Sha ruwa lita 3 kowace rana
– Kar ka hau lif, yi amfani da matakala
*Wata 3-4: Kara Karfi*
– Yi tafiya awa 1 kowace rana, ciki har da tudu
– Yi tafiya a rana (10am) sau 2 a mako don jiki ya saba da zafi
– Saka takalmin da zaka sa a Hajj — kar ka saka sabon takalmi a Makkah
– Squats sau 10 kowace rana — don bayan gida na Mina da zama a kasa
*Wata 5-6: Kamar Hajj*
– Yi tafiya 5km ba tsayawa ba, sau 3 a mako
– Yi tsaye awa 2 kana addu’a — kamar Arafat
– Koyi bacci a tabarma a kasa sau 2 a mako
*Ga Manyan Shekaru (60+):*
– Kada ka yi gudu. Yi tafiya a hankali, amma kowace rana
– Yi amfani da sanda a Hajj — Sunnah ce
– Miqe kafafu safe da yamma
– Duba BP da sugar kowace mako
*NAHCON YA KAMATA YA MAYAR DA WANNA DOLE:*
– Kowane state ya yi *Tafiyar Asabar* — 5km tare
– A duba lafiya: *Shin zaka iya tafiya 2km cikin minti 30?* Idan ba zaka iya ba, sai karin horo
– Manufa: matakai 8,000 kowace rana
> Annabi ﷺ ya ce: _”Ka amfana da lafiyarka kafin rashin lafiya.”_
Idan ka horar da jikinka yanzu, zuciyarka zata samu natsuwa don addu’a a Arafat, ba ciwon kafa ba.















