Gwamnatin jihar Legas ta baiyana aniyarta ta samar da lasisin tuƙi nata na kan ta, amma fa da haɗin gwiwa da gwamnatin taraiya.
Jaridar VANGUARD ta rawaito cewa Kwamishina Sufuri na jihar, Oluwaseun Osiyemi ne ya baiyana haka a wajen taron manema labarai na ma’aikatun jihar da ake gudanarwa duk Shekara.
Osiyemi ya yi bayanin cewa amfani da lasisin na gwamnatin jiha ba lallai ba ne, inda ya kara da cewa direba zai iya amfani da shi ko na gwamnatin taraiya.
Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin ta yi tunanin samar da nata lasisin ne don saukakawa al’umma da kuma rage matsalar samun tsaiko wajen mallakar lasisin na gwamnatin taraiya.
Ya ce idan an kammala shirin, direbobi a jihar za su rika samun lasisin tuƙi nan take ba tare da wani tsaiko ba.















