Richard Akinaka ya zama ɗan takarar jam’iyyar PDP na kujerar Sanata a mazaɓar Bayelsa ta Tsakiya gabanin zaɓen shekarar 2027.
An bayyana Akinaka a ranar Alhamis a matsayin ɗan takara ɗaya tilo a cibiyar tattara sakamakon zaɓen fidda gwani ta yankin sanatocin da ke makarantar firamare ta St. Peter’s da ke Yenagoa.
Mataimakin shugaban PDP na santoriyar kuma jami’in tattara sakamako, Mista Bidi Weris ne ya ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara bayan gudanar da zaɓen fidda gwani a sassa daban-daban na yankin.
Da ya ke jawabi bayan bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, Akinaka ya gode wa shugabannin jam’iyya da magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki bisa amincewar da suka nuna masa, inda ya bayyana takararsa a matsayin “halasci da amincewa.”
Ya kuma yi alƙawarin cewa zai mayar da hankali wajen kawo ci gaba da anfani ga al’ummar mazabarsa maimakon son rai.
Haka kuma ya tabbatar wa mambobin jam’iyyar cewa PDP za ta yi nasara a babban zaɓen, yana mai cewa jam’iyyar za ta haɗa kai domin cimma nasara.















