Dukiyar attajiri Aliko Dangote ta farfaɗo zuwa dala biliyan 36.5 bayan ya tafka gagarumar asara makon da ya gabata sakamakon faduwar kasuwar hannayen jari ta Najeriya.
A makon da ya gabata, jarin Dangote ya ragu da dala biliyan 1.2 a zango guda na hada-hadar kasuwar hannun jari, galibi saboda faduwar farashin hannun jarin Kamfanin Dangote Cement da kashi 10%.
Duk da sauye-sauyen da ake samu a kasuwar hannayen jari, Kamfanin Dangote Cement da sauran kamfanonin Dangote na ci gaba da kasancewa cikin haɓaka tare da ci gaba da samun kyawawan sakamakon kasuwanci.
Ana sa ran Dangote zai samukusan dala miliyan 490 daga rabon ribar (dividend) da Kamfanin Dangote Cement zai biya nan ba da jimawa ba, wanda zai zama mafi yawan kaso daga jimillar dala miliyan 564 da za a raba wa masu hannayen jari.















