Wani rahoto da aka fitar a ƙasar Saudiyya ya baiyana cewa mutane sama da miliyan 4.4 ne ke aiki a ɓangaren harkar gine-gine a ƙasar, kamar yadda hukumar kula da ƴan kwangila ta baiyana.
Rahoton ya ce adadin ma’aikatan ya sanya ɓangaren gine-gine ya zama ɗaya daga cikin ma’aikatu da su ka fi ɗaukar ma’aikata.
Hukumar, a wani sabon rahoto da ta fitar ta ce akwai kamfanonin gine-gine sama da dubu 20 a 2025 a ƙasar, inda darajar kamfanonin ta haura tiriliyan 3.
ADVERTISEMENT
Rahoton ya ce a cikin wannan dama da miliyan 4.4 ɗin, ƴan asalin Saudiyya su dubu 581,843 ne, inda hakan ke nuni da kashi 14% na adadin ma’aikatan ɓangaren gine-gine a ƙasar.
















