Biz Point
  • Home
  • News
  • National
  • Business News
  • Forex
  • Tech
  • Entertainment
  • HAUSA
  • More
    • About Us – Biz Point
    • Contacts
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
No Result
View All Result
  • Home
  • News
  • National
  • Business News
  • Forex
  • Tech
  • Entertainment
  • HAUSA
  • More
    • About Us – Biz Point
    • Contacts
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
No Result
View All Result
Biz Point
No Result
View All Result
Home Hausa

Gidan Talabijin, Matashiya TV zai gudanar da gasar masu ƙananan sana’o’i a Kano

BizPoint by BizPoint
August 4, 2026
in Hausa
0
Gidan Talabijin, Matashiya TV zai gudanar da gasar masu ƙananan sana’o’i a Kano
0
SHARES
2
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Gidan Talabijin na Matashiya TV à jihar Kano ya sanar da gudanar da gasar masu ƙananan sana’o’i a jihar.

Tuni ma Matashiya TV ya sanar da ce hamshakin dan kasuwar nan, shugaban rukunin kamfanonin Ammasco Alhaji Mustapha Ado Muhammad ya sha alwashin bayar da gagarumar gudunmawa a gasar masu ƙananan sana’o’i da Matashiya TV ta shirya gudanarwa a watan Agustan 2026.

Alhaji Mustapha ya tabbatar da wa shugaban Matashiya TV Abubakar Murtala Ibrahim cewar zai shiga cikin domin ƙarfafawa matasa da masu ƙananan sana’o’i yadda za a ƙarfafa musu gwiwa.

ADVERTISEMENT

Ya ce matasa su ne ƙashin bayan al’umma kuma da ma can manufarsa da dukkan ayyukan da ya ke yi a kullum ya na ƙoƙarin yin wani abu da zai samar da aikin yi a tsakanin matasa.

A ranar da za a gudanar da gasar zai bayar da mota mai ɗauke da allon majigi don haska yadda gasar za ta kasance.

Ya ce wannan ba ƙaramin yunƙuri ba ne domin hakan zai taimakawa masu ƙananan sana’o’i domin su san cewar su na yin wani abu mai kyau da za a yaba kuma a girmamashi.

Ya ƙara da cewar hakan zai sa matasa su karkata wajen rungumar sana’o’i wanda hakan zai kawo ƙarshen matsalar tsaro da a ke fuskanta a ƙasar.

Har yanzu damar shiga gasar a buɗe ta ke ga duk masu buƙata za su iya tuntuɓar lamba https://wa.me/2348096399266 don kasancewa a ciki.

Ga ƙarin bayani a kai.

Ka na da ƙwarewa da gogewa a kan wata sana’a ta hannu? Ki na da ƙwarewa da gogewa a kan wata sana’a ta hannu

Matashiya TV za ta gudanar da gasar sana’o’in hannu a watan Agustan shekarar 2026 a wani ɓangare na bikin cika shekara 10 da kuma ƙarfafawa matasa don su tsaya da ƙafarsu.

Za a bayar da kyautuka ga waɗanda su ka yi fice daga na ɗaya zuwa na uku, sannan za a bayar da shaida ga waɗanda su ka shiga gasar.

Dama ce ga matasa maza da mata sannan daga ko ina a Najeriya, amma ku sani waɗanda za su zo daga wajen Kano za su ɗauki nauyin kansu.

Za ku iya aikawa da sunanku, adireshi da sana’ar da ku ka ƙware a cikinta a whatsappa https://wa.me/2348096399266
Za a rufe ranar Juma’a 7/8/2026.

Share this:

  • Share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Share on X (Opens in new window) X

Ad 2
Tags: Hausa
ADVERTISEMENT
Previous Post

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano na kiran maniyyatan da su ka yi rijistar Hajjin baɗi da su kai mata fasfunan su

BizPoint

BizPoint

Related Posts

Kashi 14% ne na ƴan asalin Saudiyya ke aikin ƙarfi a ƙasar – Rahoto
Hausa

Kashi 14% ne na ƴan asalin Saudiyya ke aikin ƙarfi a ƙasar – Rahoto

August 1, 2026
Tsohon shugaban ƙaramar hukuma ya koma sana’arsa ta ɗinki bayan kotu ta sauke shi daga mukamin sa a Kano
Hausa

Tsohon shugaban ƙaramar hukuma ya koma sana’arsa ta ɗinki bayan kotu ta sauke shi daga mukamin sa a Kano

July 29, 2026
Bangladesh ta sanar da kudin aikin Hajjin 2027 tare da yin ragin kuɗin tikitin jirgi ga alhazai
Hausa

Bangladesh ta sanar da kudin aikin Hajjin 2027 tare da yin ragin kuɗin tikitin jirgi ga alhazai

July 23, 2026
Kayayyakin da Nijar ke fitarwa zuwa China sun ƙaru da kashi 100
Hausa

Kayayyakin da Nijar ke fitarwa zuwa China sun ƙaru da kashi 100

July 21, 2026
Gobarar Kasuwar Singa: Gwamnan Kano ya tabbatar ana daf da bamu tallafin N8b da akai mana alƙawari – Zakari
Hausa

Gobarar Kasuwar Singa: Gwamnan Kano ya tabbatar ana daf da bamu tallafin N8b da akai mana alƙawari – Zakari

July 19, 2026
Gwamnatin Kano ta turawa mazaunin jihar Neja N5.3m kuɗin giratuti bisa kuskure
Hausa

Gwamnatin Kano ta turawa mazaunin jihar Neja N5.3m kuɗin giratuti bisa kuskure

July 18, 2026
ADVERTISEMENT

Stay Connected test

  • 23.9k Followers
  • 99 Subscribers
ADVERTISEMENT
  • Trending
  • Comments
  • Latest
RE: From NEPU to Asara — By Ibrahim Bello Kano

RE: From NEPU to Asara — By Ibrahim Bello Kano

August 21, 2025
UPDATED: Kano gov announces date for implementation of new minimum wage

UPDATED: Kano gov announces date for implementation of new minimum wage

October 29, 2024
Petrol subsidy hits N2.57tr as supply rises by 10%

JUST IN: Tinubu considering partial reversal of fuel subsidy on petrol

August 15, 2023
How Katsina oil mogul ordered arrest of man over social media post

How Katsina oil mogul ordered arrest of man over social media post

July 15, 2024

Hello world!

1

5 dead, 4 rescued in canoe mishap

0

Naira weakens again, down by 0.29 percent

0

UBA Foundation opens portal for 2022 essay competition, announces prizes

0
Gidan Talabijin, Matashiya TV zai gudanar da gasar masu ƙananan sana’o’i a Kano

Gidan Talabijin, Matashiya TV zai gudanar da gasar masu ƙananan sana’o’i a Kano

August 4, 2026
Why we are yet to announce 2027 Hajj deposit – Kano pilgrims board

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano na kiran maniyyatan da su ka yi rijistar Hajjin baɗi da su kai mata fasfunan su

August 4, 2026
Gov. Yusuf commissions health projects in Kano

Gov. Yusuf commissions health projects in Kano

August 4, 2026
Don’t betray public trust, Kano Commissioner tasks journalists on vidence-based, accurate health reporting

Don’t betray public trust, Kano Commissioner tasks journalists on vidence-based, accurate health reporting

August 2, 2026

Recent News

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Biz Point

© 2024 Biz Point

Navigate Site

  • Home
  • About Us
  • Contacts
  • Disclaimer
  • Privacy & Policy
  • Terms & Conditions

Follow Us

No Result
View All Result
  • Home
  • News
  • National
  • Business News
  • Forex
  • Tech
  • Entertainment
  • HAUSA
  • More
    • About Us – Biz Point
    • Contacts
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions

© 2024 Biz Point