Gidan Talabijin na Matashiya TV à jihar Kano ya sanar da gudanar da gasar masu ƙananan sana’o’i a jihar.
Tuni ma Matashiya TV ya sanar da ce hamshakin dan kasuwar nan, shugaban rukunin kamfanonin Ammasco Alhaji Mustapha Ado Muhammad ya sha alwashin bayar da gagarumar gudunmawa a gasar masu ƙananan sana’o’i da Matashiya TV ta shirya gudanarwa a watan Agustan 2026.
Alhaji Mustapha ya tabbatar da wa shugaban Matashiya TV Abubakar Murtala Ibrahim cewar zai shiga cikin domin ƙarfafawa matasa da masu ƙananan sana’o’i yadda za a ƙarfafa musu gwiwa.
Ya ce matasa su ne ƙashin bayan al’umma kuma da ma can manufarsa da dukkan ayyukan da ya ke yi a kullum ya na ƙoƙarin yin wani abu da zai samar da aikin yi a tsakanin matasa.
A ranar da za a gudanar da gasar zai bayar da mota mai ɗauke da allon majigi don haska yadda gasar za ta kasance.
Ya ce wannan ba ƙaramin yunƙuri ba ne domin hakan zai taimakawa masu ƙananan sana’o’i domin su san cewar su na yin wani abu mai kyau da za a yaba kuma a girmamashi.
Ya ƙara da cewar hakan zai sa matasa su karkata wajen rungumar sana’o’i wanda hakan zai kawo ƙarshen matsalar tsaro da a ke fuskanta a ƙasar.
Har yanzu damar shiga gasar a buɗe ta ke ga duk masu buƙata za su iya tuntuɓar lamba https://wa.me/2348096399266 don kasancewa a ciki.
Ga ƙarin bayani a kai.
Ka na da ƙwarewa da gogewa a kan wata sana’a ta hannu? Ki na da ƙwarewa da gogewa a kan wata sana’a ta hannu
Matashiya TV za ta gudanar da gasar sana’o’in hannu a watan Agustan shekarar 2026 a wani ɓangare na bikin cika shekara 10 da kuma ƙarfafawa matasa don su tsaya da ƙafarsu.
Za a bayar da kyautuka ga waɗanda su ka yi fice daga na ɗaya zuwa na uku, sannan za a bayar da shaida ga waɗanda su ka shiga gasar.
Dama ce ga matasa maza da mata sannan daga ko ina a Najeriya, amma ku sani waɗanda za su zo daga wajen Kano za su ɗauki nauyin kansu.
Za ku iya aikawa da sunanku, adireshi da sana’ar da ku ka ƙware a cikinta a whatsappa https://wa.me/2348096399266
Za a rufe ranar Juma’a 7/8/2026.















