Gwamnatin Jihar Taraba ta rage albashin ma’aikatan shirin Operation Keep Taraba Clean, wanda aka fi sani da masu share tituna, daga naira 15,000 zuwa naira 10,000, tana mai cewa hakan zai ba ta damar biyan sabbin ma’aikatan gwamnati da aka ɗauka aiki a jihar nasu albashin.
Shugaban Hukumar Kula da Muhalli da Tsaftar Jihar Taraba, Illiya Kefas ne ya tabbatar da wannan mataki yayin da yake zantawa da manema labarai a Jalingo.
A cewarsa, an ɗauki wannan mataki ne bisa umarnin Gwamna Agbu Kefas domin gudanar da albarkatun da ake da su yadda ya kamata, sakamakon ɗaukar sabbin ma’aikatan shara na jiha da ƙananan hukumomi.

Sai dai a watan Maris na shekarar 2024, rahotanni sun baiyana cewa an bukaci ma’aikatan su amince da ragin albashi na naira 5,000 ko kuma su rasa ayyukansu, lamarin da albashinsu na wata-wata ya kom naira 15,000.
Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan sun karɓi naira 10,000 a watan Mayun 2026, wanda ke nuna wani ƙarin ragin albashi daga adadin da aka cimma yarjejeniya a kai a baya.
Da ya ke bayyana dalilin ɗaukar wannan mataki, Kefas ya ce gwamnatin jihar ta wajabta daidaita nauyin kuɗaɗen da ke kanta bayan ɗaukar dimbin sabbin ma’aikata aiki.















