Wani Alaramma, Malam Sagir Shu’aibu Bunkure ya zargi shugaban ƙaramar hukumar ta Bunkure, Aliyu Bashir Barkum da ƙwace masa kujerar aikin Hajjin baɗi da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bashi.
Freedom Radio ta rawaito cewa Malam Sagir ya ce tuni masoya da muridai su ka riƙa ruwa su na taya shi murna amma kwatsam sai magana ta canja, inda ya ce an canja sunan sa da wani.
” Shugaban ƙaramar hukumar Bunkure, Alhaji Bashir Barkum ya kira ni ya yi min albishir ce min gwamna ya bani kujerar aikin Hajji. Na yi godiya sosai.
” Kwatsam kuma sai ya kira ni ya ke fada min cewa an janye kujerar nan ta aikin Hajji. Shi ne na ke tambaya cewa gwamnan ne ya fasa ko kuma wani abu ne ya faru? Na san dai gwamna mai adalci ne. Shine na ke so na ji yadda aka haihu a ragaya,”
Da Freedom Radio ta tambayi shugaban ƙaramar hukumar, ya yi bayanin cewa asali kujerar shugaban Ulama gwamna ya ce a baiwa.
Ya kara da cewa ganin cewa akwai ƴan rikice-rikice tsakanin Ulama din kuma babu wani tsayayyen shugabanci, shi ne sai ya zaci kujerar ta alarammomi ce kuma Malam Sagir shine shugaba.
” Daga bisani sai mu ka gano cewa ashe gwamnan alarammomi masu saukar Alkur’ani tun asali a Miller Road ya ke nufi, shi ne na fada masa abinda ya faru. Amma ba ƙwace masa na yi ba. Dama can ba ta shi ba ce,” in ji shugaban ƙaramar hukumar.















