Kotu ta ɗaure wasu dilolin sholisho guda biyu, Kabiru Isa (Mada) da Usman Hamisu (Mani), bisa baiwa yara har guda 43 kayan maye a matsayin ladan aike a jihar Kano.
Shugaban kwamitin Kar-ta-Kwana na yaƙi da shaye-shaye da dabanci a jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin-Gado ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a jihar Kano a ranar Talata.
A cewar Rimin-Gado, matasan na baiwa yaran, waɗanda ke sana’ar jari-bola, sholisho da sauran kayan maye a matsayin ladan aikinsu, maimakon su basu kuɗin.
Ya ce tuni kwamitin ya ceto yaran su 43 tun daga lokacin, kuma an yi musu gwaje-gwajen lafiya.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu suna samun shawarwari da kulawar, yayin da kwamitin ke ci gaba da neman iyayen su.
“An riga an gano wasu daga cikin iyayen kuma an haɗa su da ’ya’yansu,” in ji Rimin-Gado.
Rimin-Gado ya kara da cewa tun bayan kafa kwamitin a watanni biyu da su ka gabata, ya samu nasarar kama mutane 380 da kuma ɗaure 230 a kurkuku.















