Kamfanin Nestlé Milo, tare da haɗin gwiwar tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, ya shirya gasar ƙwallon ƙafa ta yara ’yan ƙasa da shekaru 13 a Kano.
Gasar, wadda ta gudana na tsawon kusan makonni uku, ta haɗa ƙungiyoyi sama da 16 daga sassa daban-daban, da nufin gano yara masu baiwar ƙwallon ƙafa da kuma ba su horo da damar haɓaka ƙwarewarsu.
Da ya ke jawabi a wajen buɗe gasar, wakilin kamfanin Milo, Gilbert Tweneboah-Koduah, ya ce shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin kamfanin na amfani da wasanni wajen bunƙasa baiwar yara, tare da koya musu muhimmancin jajircewa da sadaukarwa.
Ya ce duk da cewa an samu zakara a gasar, babban abin da aka mayar da hankali a kai shi ne gano yara masu hazaka daga cikin waɗanda su ka fafata, tare da fatan mayar da gasar wani shiri na shekara-shekara.
Shi ma Ahmed Musa, wanda ke matsayin jakadan Milo, ya ce an shirya gasar ne domin farfaɗo da sha’awar yara ga ƙwallon ƙafa da kuma ba masu baiwa damar samun horo da tallafin da zai taimaka musu wajen cimma burinsu.
Ahmed Musa ya ce irin wannan dama ce ta taimaka masa a lokacin yana ƙarami, yana mai bayyana fatan cewa daga cikin yaran da suka fafata za a samu waɗanda za su wakilci Najeriya a manyan gasanni nan gaba.
A nasa bangaren, Manajan filin wasan Ahmed Musa, Musa Muhammad, ya ce an shirya gasar ne domin ba yara masu shekaru tsakanin takwas zuwa 13 damar shiga fafatawa, musamman ganin cewa yawancin gasannin ƙwallon ƙafa ana shirya su ne ga manya.
Ya ce a ƙarshen gasar, Khamis Boy ta zo ta farko, yayin da BC Academy ta zo ta biyu, sai Legacy da ta zo ta uku. Kungiyoyin sun samu kyaututtukan kuɗi daban-daban.
Manajan Khamis Boy ya bayyana cewa ƙungiyarsu ta samu kyautar naira miliyan ɗaya, yana mai godiya ga Milo da Ahmed Musa bisa samar da damar da ta bai wa yaran damar fafatawa da nuna bajintarsu.
Shi ma Manajan Milo na shiyyar Arewa maso Yamma, Dayo Adetoya, ya ce haɗin gwiwar kamfanin da Ahmed Musa na da nufin gano yara masu baiwa tare da tallafa musu wajen ƙarfafa mafarkinsu na zama ƙwararrun ’yan ƙwallo.
Ya ce gasar ta ba su damar gano yara da dama masu hazaka, kuma kamfanin zai duba hanyoyin da zai ci gaba da tallafa musu ta hanyar horo da sauran abubuwan da za su taimaka wajen haɓaka ƙwarewarsu.















