Shugaban tashar Rahma Radio da TV Abuja, Malam Nafiu Yahaya, ya ajiye aikinsa.
Nafiu Yahaya shi ne mutum na farko da ya fara magana a Rahma Radio Kano lokacin da aka buɗe tashar a shekarar 2011, sannan ya kasance cikin waɗanda suka fara gudanar da Rahma Radio Abuja a shekarar 2021.

ADVERTISEMENT
A tsawon lokacin da ya yi yana aiki a tashoshin biyu, ya riƙe manyan sassa da mukamai daban-daban.
Ya kuma gode wa Shugabar Hukumar Zartarwa ta tashoshin, da sauran abokan aikinsa, bisa kyakkyawar zaman tare da suka yi na tsawon shekaru goma sha biyar.
















