Hukumar Kula da Sufuri ta ƙasar Saudiyya (TGA) ta sanar da korar wasu ƴan kasashen waje uku daga kasar, bayan da aka same su da laifin yin haya da motocin da ba na haya ba kuma ba mai lasisin tuƙi a cikin su.
Hukumar ta ce an kuma ci tarar su ukun jimillar Riyal dubu 35,000 na Saudiyya.
Biyu daga cikin wadanda aka kama, ɗaya ɗan ƙasar Egypt da ɗan ƙasar Indiya, an same su da laifin jigilar fasinjoji da motocin kansu ba tare da samun lasisin da ya dace ba.
An ci tarar kowannensu Riyal 12,000, tare da bayar da umarnin ficewa daga Saudiyya.
Shi kuwa mutum na uku, dan kasar Chadi, an ci shi tarar Riyal 11,000, sannan aka bayar da umarnin korarsa daga kasar.
A cewar Hukumar TGA, laifin da dan Chadin ya aikata shi ne yana shirin ɗaukar fasinjoji da motarsa ba tare da lasisi ba.
Hukumar ta jaddada cewa gudanar da ayyukan jigilar fasinjoji ba tare da lasisin da ake bukata ba, ya saba wa dokokin Saudiyya.















