Birtaniya ta tabbatar da barkewar cutar mashashsharar kifi mai suna Koi Herpesvirus a wani gidan gona da ake kiwon kifi.
Birtaniya ta tabbatar da bullar cutar ta Koi Herpesvirus (KHV) a wata cibiyar kiwon kifi da ke unguwar Aspley Guise, yankin Milton Keynes, tare da kakaba dokokin takaita zirga-zirgar dabbobin ruwa domin hana yaduwar cutar.
Hukumar Binciken Lafiyar Kifi ta Birtaniya (Fish Health Inspectorate) ta tabbatar da barkewar cutar a wani gidan gona da ake kiwon kifi da ke Tree Farm, Aspley Guise, a ranar 10 ga Satumba, kamar yadda wata sanarwa da gwamnatin Birtaniya ta wallafa ranar Litinin ta bayyana.
Cibiyar Nazarin Muhalli, Kamun Kifi da Kimiyyar Kiwon Dabbobin Ruwa (Centre for Environment, Fisheries and Aquaculture Science) wadda ta wallafa sanarwar, ta bayyana cewa cutar KHV “mummunar cuta ce ta kwayar cuta da ke addabar kifi, kuma tana cikin jerin cututtukan da aka sanya wa ido a Birtaniya.”
Ta ce cutar na shafar dukkan nau’o’in kifi irin su carpi (Cyprinus carpio), kuma tana iya haddasa mutuwar kifaye da dama cikin gajeren lokaci.














