Biz Point
  • Home
  • News
  • National
  • Business News
  • Forex
  • Tech
  • Entertainment
  • HAUSA
  • More
    • About Us – Biz Point
    • Contacts
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
No Result
View All Result
  • Home
  • News
  • National
  • Business News
  • Forex
  • Tech
  • Entertainment
  • HAUSA
  • More
    • About Us – Biz Point
    • Contacts
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
No Result
View All Result
Biz Point
No Result
View All Result
Home Hausa

Dangote zai raba hannun jarin IPO kyauta ga mata miliyan 2 da mazajensu su ka rasu a Arewa

BizPoint by BizPoint
September 26, 2026
in Hausa
0
Dangote zai raba hannun jarin IPO kyauta ga mata miliyan 2 da mazajensu su ka rasu a Arewa
0
SHARES
2
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Mamallakin Matatar Man Dangote, Alhaji Aliko Dangote zai raba hannun jarin matatar da ya ƙaddamar, mai suna IPO, kyauta ga mata miliyan biyu da mazajensu su ka rasu.

Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa, wato Arewa Consultative Forum, ACF, reshen jihar Kano, Goni Farouk Umar ne ya baiyana hakan a wajen taron wayar da kan jama’ar jihar akan alfanon hannun jari, wanda ya gudana a yau Asabar a shelkwatar kungiyar a Kano.

Gwani Umar Farouk

ADVERTISEMENT

A cewar Goni Umar, Dangote zai raba kyautar hannun jari ne ga matan da suka rasa mazajen su, musamman a jihohin Borno, Adamawa, Yobe, Katsina, Zamfara da Sokoto da sauran su.

Ya kara da cewa wannan tagomashi zai taimaka matuka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihohin, musamman waɗanda su ke fama da aiyukan ƴan ta’adda.

Hakazalika a yayin taron, Goni Umar ya baiyana cewa zai saya wa abokan karatun sa na Makarantar Rumfa, mutane 60 hannun jarin, inda a yau din ma da dama su ka zo aka dauki bayanan su.

Haka kuma kungiyar ta ACF ta allafawa mutane wajen taimaka musu wajen siyan hannun jarin tare da buɗe musu asusun ajiya na banki da zai basu damar siyan hannun jarin.

Some of the beneficiaries being registered.

Da ya ke jawabi, Umar ya ce sun zakulo masu ƙaramin karfi a cikin al’umma domin taimaka musu wajen mallakar hannun jarin na Dangote, inda ya bayyana cewa dama can ƙungiyar na tallafawa mabukata a lokuta daban-daban.

Ya kara da cewa kamar yadda Dangote ya kira suna hannun jari da cewa hannun jari ne na al’umma, wannan dalili ne ya sa ACF a Kano ta ga dacewar sayawa masu ƙaramin ƙarfi domin su amfana.

Goni Umar ya kuma musanta zargin da wasu ke yi na cewa ba za a samu riba daga hannun jarin na Dangote ba, inda ya zayyano ribar da kamfanin ya samu a fannin siminti da sukari da ita kanta matatar man.

Share this:

  • Share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Share on X (Opens in new window) X

Ad 2
Tags: Hausa
ADVERTISEMENT
Previous Post

Romo, a Kano farming village where wives buy fertilizer for husbands

BizPoint

BizPoint

Related Posts

UNGA: Wata jiha a Arewacin Nijeriya ta yi baje-kolin damar zuba jari a harkar ƙaro, riɗi da sauran su
Hausa

UNGA: Wata jiha a Arewacin Nijeriya ta yi baje-kolin damar zuba jari a harkar ƙaro, riɗi da sauran su

September 23, 2026
An kammala gasar ƙwallon ƙafa da Nestlé Milo ya shirya a Kano
Hausa

An kammala gasar ƙwallon ƙafa da Nestlé Milo ya shirya a Kano

September 23, 2026
Kotu ta ɗaure dilolin sholisho 2 bisa baiwa yara kayan maye a matsayin ladan aike a Kano
Hausa

Kotu ta ɗaure dilolin sholisho 2 bisa baiwa yara kayan maye a matsayin ladan aike a Kano

September 22, 2026
Mutane 48 sun mutu sakamakon shan tsumin maganin gargajiya
Hausa

Mutane 48 sun mutu sakamakon shan tsumin maganin gargajiya

September 19, 2026
Farashin ɗanyen mai ya sake sauka bayan da Saudiyya ta nemo wata hanyar safarar sa
Hausa

Farashin ɗanyen mai ya sake sauka bayan da Saudiyya ta nemo wata hanyar safarar sa

September 18, 2026
YANZU-YANZU: Sarki Sanusi ya gargaɗi al’ummar Kano akan hannun jarin Matatar Man Dangote
Hausa

YANZU-YANZU: Sarki Sanusi ya gargaɗi al’ummar Kano akan hannun jarin Matatar Man Dangote

September 17, 2026
ADVERTISEMENT

Stay Connected test

  • 24k Followers
  • 99 Subscribers
ADVERTISEMENT
  • Trending
  • Comments
  • Latest
RE: From NEPU to Asara — By Ibrahim Bello Kano

RE: From NEPU to Asara — By Ibrahim Bello Kano

August 21, 2025
UPDATED: Kano gov announces date for implementation of new minimum wage

UPDATED: Kano gov announces date for implementation of new minimum wage

October 29, 2024
Petrol subsidy hits N2.57tr as supply rises by 10%

JUST IN: Tinubu considering partial reversal of fuel subsidy on petrol

August 15, 2023
How Katsina oil mogul ordered arrest of man over social media post

How Katsina oil mogul ordered arrest of man over social media post

July 15, 2024

Hello world!

1

5 dead, 4 rescued in canoe mishap

0

Naira weakens again, down by 0.29 percent

0

UBA Foundation opens portal for 2022 essay competition, announces prizes

0
Dangote zai raba hannun jarin IPO kyauta ga mata miliyan 2 da mazajensu su ka rasu a Arewa

Dangote zai raba hannun jarin IPO kyauta ga mata miliyan 2 da mazajensu su ka rasu a Arewa

September 26, 2026
Romo, a Kano farming village where wives buy fertilizer for husbands

Romo, a Kano farming village where wives buy fertilizer for husbands

September 26, 2026
How KCPC resolved dispute between firm, customer over purchase of motorbike

How KCPC resolved dispute between firm, customer over purchase of motorbike

September 25, 2026
At MAN AGM in Kano, manufacturers throng Dangote pavilion over Peoples IPO

At MAN AGM in Kano, manufacturers throng Dangote pavilion over Peoples IPO

September 25, 2026

Recent News

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Biz Point

© 2024 Biz Point

Navigate Site

  • Home
  • About Us
  • Contacts
  • Disclaimer
  • Privacy & Policy
  • Terms & Conditions

Follow Us

No Result
View All Result
  • Home
  • News
  • National
  • Business News
  • Forex
  • Tech
  • Entertainment
  • HAUSA
  • More
    • About Us – Biz Point
    • Contacts
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions

© 2024 Biz Point