Hukumar Gasar Premier ta ce ta gano cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta aikata manyan laifuka na karya dokokin hada-hadar kuɗaɗe a gasar na tsawon shekaru tara.
Hukumar ta tabbatar da hakan ne bayan wani kwamitin bincike mai zaman kansa da hukumar ta kafa ya tabbatar da cewa ƙungiyar ta yi amfani da wasu yarjejeniyoyin kasuwanci na bogi domin ƙara yawan kuɗaɗen shigarta da kuma rage kuɗaɗen da take kashewa da sama da fam miliyan 900.
Premier League ta sanar da sakamakon binciken a ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026, bayan ta wallafa wani sashe da aka cire wasu bayanai daga cikin cikakken hukuncin Hukumar Binciken.
Kwamitin ya samu Manchester City da laifin dukkan zarge-zargen da suka shafi manyan laifukan take dokokin kuɗi, da kuma mafi yawan zarge-zargen da suka shafi gazawar ƙungiyar wajen baiwa hukumar haɗin kai a lokacin binciken.
Binciken ya shafi kakar wasanni daga 2009/10 zuwa 2017/18.
A cewar Premier League, kwamitin binciken ya gano cewa City ta shirya wasu “yarjejeniyoyin bogi” da wasu abokan hulɗarta na kasuwanci, inda aka bayyana yarjejeniyoyin ba kamar yadda aka amince da su a zahiri ba.
A game da hukuncin da ta tanadar wa City, hukumar ta ce shima wannan batu na hukunci za a yi masa zama na musamman da a ga irin hukuncin da ya dace a yanke wa Man City din.















