Hoto na farko; Ayaba ce da muke siya daga kudancin kasar nan. A motocin J5 ake dauko mana ita, sannan a mafi yawan lokutan akan dauki kwanaki biyu, wasu lokutan aka samu mechanical problem har kwana biyar ana yi. Kuma a haka, za tazo lafiya kalau, kadan ne take samun matsala. Daga wajena, zan dora a Mota zuwa Niger republic wanda za’a dauki wasu kwanakan a hanya, amma duk da haka, cikin ikon Allah, kayana suna sauka lafiya kalau, fresh and strong.
Hoto na biyu; Ayaba ce irin ta mu wacce ake nomawa anan arewacin kasar nan. Tana da zaki sosai, amma idan muka siyo ta daga gona zuwa kasuwa ba za’a wuce awanni ba, ta jima sosai wuni daya, amma zaiyi matukar wahala a kwana.
Daga gona kai tsaye na dora a mota zuwa Niger republic wanda duka tafiyar kwana biyu ce, amma duba ku gani yadda ta zama. Wasu lokutan, tun a wajenmu take canjawa, shiyasa mafi yawan lokuta idan aka siyo Ayaba irin wannan, muke gaggawar rabuwa da ita, saboda a kowanne dakika cikin hatsari muke. Ana yi mun tallar ta sosai, amma tsoro ke hanani.
Akwai mutane da yawa da suka tambayeni meye ake samun wannan banbancin? Ina tunanin akwai banbanci sosai tsakanin Ayabar Kudu da ta Arewa. Life span ba daya bane, juriya da karfinn su ba daya ba.
Maybe daga seedling ne, ko kuma daga kasar noman. Na yi wannan rubutun ne domin in jawo hankalin wadanda suke da sha’awar noman Ayaba anan arewacin kasar nan, da suyi bincike su gano meye dalilin da yasa, Ayabarmu ta banbanta da ta su? Wannan ba karamin gap bane da ya kamata a nemo kwararrun masu bincike, domin gano dalilai da kuma mafita. Life span yana da matukar alfanu ga kayan fruits.
Domin idan za’a siyar mun da ton goma na Ayabar arewa a 1m, zan iya siyan ta kudu a 3m saboda wannan life span din. Akwai sauki sosai, amma wannan saukin yana da price, wanda ‘yan kasuwa irinmu ba za su iya biya ba. masu siya don su ci, ko wadanda za su siyar da ita a bonanza a cikin birni da kauyuka sun fi samun riba, amma ba irinmu wanda muke tura kaya nesa ba. Dole ta sa muka hakura.
©️Abdulhadi Dankama
01 October, 2026















